RAMA ALKHAIRI DA ALKHAIRI

 AN GUDANAR DA DUBA MARASSA DA BASU MAGUNGUNA KYAUTA A GARIN KUNYA. 


Ƙungiyar ALHAJI JATAU ISLAMIC CENTRE AJIC tare da hadin gwuiwar ƙungiyoyin


KUNYA HEALTH FORUM K. H. F

KUNYA SOCIAL MEDIA INFLUENCER K. S. M. I

KUNYA EDUCATIONAL FOUNDATION K. E. F

KUNYA CONCERN FORUM KUCOF


Duk a cikin bikin taya murnar kafuwar wannan gidauniya ta AJIC shekara guda da kafuwa. 

Ita dai wannan cibiya an samar da ita ne musamman domin ayyukan da suka shafi taimako da cigaban al'umma, wanda ya ƙirƙiro wannan gidauniya wato Pharm. Dr. Ibrahim Jatau ya bayyana cewar ya ƙirƙiri wannan gidauniya ne domin taimakawa yan'uwan shi musulmi. 


A shekarar farko an gudanar da bikin buɗe masallachin Kamsu-salawat wanda aka kira masallachin da sunan HAJIYA INNA MOSQUE, sannan an gudanar da duba marasa lafiya da basu magunguna kyauta da kuma wasu manyan gwaje-gwaje da suka shafi lafiya. 


A wannan karon da gidauniya ta cika shekara cif da kafuwa an sake maimaita duba marasa lafiya da kuma basu magunguna inda a wannan karon akwai fannonin kiwon lafiya da aka ƙaro kamar su


Likitocin Haƙora wato Dentist

Likitoci masu kula da Mata wato Gynea

Likitoci masu kula da Jinya wato Nurses

Likitoci masu duba marasa lafiya wato Consultants

Likitoci masu kula da gwajin jini wato Scientists

Likitoci masu kula da tsaftar muhalli wato Environmentalist

Likitoci masu kula da fannin magunguna wato Pharmacists

Da sauran rukunonin kiwon lafiya wanda duk daga cikin garin Kunya ne suka fito domin nuna godiyar su ta hanyar sadaukar da iliminsu domin taimakon al'ummar su. 


Muna addua Allah ya sakawa da dukkan wadanda suka dau nauyi ko suka taimaka da gudunmawarsu ta kowanne fanni da Alkhairi, buƙatunmu na Alkhairi Allah ya biya mana, Allah ya sanya mana ladan a mizani ya kuma gafarta mana ya sanya muyi kyakkyawan ƙarshe ameen. 




Previous Post Next Post