Mai HANKALI...
Ban fi minti biyar da fitowa daga cikin kantin ba, ina tsaye bakin titi ina jiran a-daidaita-sahu, sai ga wata 'yar yarinya da ba ta wuce shekaru bakwai ba, ta tsaya gabana ta ce, "Anti, ki taimaka mini da sadaka in ci abinci."
Na dube ta na yi murmushi, cikin wasa na ce mata, "ni ma ban ci abinci ba tun safe, yunwa nake ji."
Ta dube ni cike da mamaki ta ce, "Da gaske?"
Na gyaɗa kai, "Eh."
Sai na ga ta kwance ɗaurin zaninta, ta ciro kuɗi ta miƙo mini, ta ce, "Ungo wannan ki ci abinci."
Na karɓa na ƙirga, sai na ga naira ɗari da hamsin. Na dube ta na ce, "Wannan ba zai ishe ni cin abinci ba."
Sai ta sake ƙwaƙulo wasu kuɗin ta ba ni, ta ce, "Ga cikon hamsin nan, su ke nan kuɗina. Abincin jaka guda dai ya ishe ki. Ki shiga wancan lungun akwai wata mai sayar da shinkafa da wake da araha."
Na dubi 'yar yarinyar nan ina ta mamaki. Don na ƙara latsa ta, sai na ce, "To idan na ci abinci, da wane kuɗin kuma zan sayi ruwan da zan sha."
Sai ta ce, "Jira ni."
Sai na ga ta tafi gun mutane ta fara bara. Zuwa can ta dawo riƙe da murtala ta miƙa mini. Ta ce, "Karɓi wannan ki sayi fiyawota."
Na karɓa ina ta mamaki. Can sai na tambayi yarinyar, "Ke kuwa me ya sa kika ba ni duka kuɗinki domin na ci abinci."
Ta kada baki ta ce, "Saboda zan kuma yin bara in samu wasu. Ke kuma na tabbata ba za ki iya yin bara ba, komai yunwar da kike ji, babu wanda zai san halin da kike ciki."
Wannan amsa, ta nuna tausayawa ga ɗan Adam, da ta fito daga bakin 'yar ƙaramar yarinya, ta burge ni ta kuma sanya ni ƙwalla. Na ce a raina, ina ma haka duka halayen mutane suke, wajen nuna tausayi ga junansu, da duniya ta zauna lafiya.
Na mayar mata da kuɗinta, na kuma ɗebo wasu daga cikin jakata na ba ta, na ce ta tafi gida, su ci abinci ita da iyayenta.
Har na isa gida ban daina tunani tare da mamakin hankalin wannan 'yar yarinya ba. Hausawa suka ce, mai hankali shi ke ba kaza ruwa ga damina.
Bukar Mada
04/05/2023