SHAYE - SHAYE A TSAKANIN MATASAN AREWA ( 15-45 years )
Mun shgo wani yanayi da gurbacewar dabi'un matasan arewa a kullum ke qara gurbacewa ta fuskar Ta'ammali da kayan maye ko in ce shaye shaye, kama daga kan magungunan turawa, xuwa ganye da sauran abubuwan bugarwa wanda ake sarrafa su da abubuwan yau da kullum.
A matsayin ka na matashi kamata yae ace naxari da tunaninka ya tafi ixuwa hangen hanyar da xaka samar domin cigaban rayuwarka da rayuwar iyalin ka.
Ba sae wani yace maka abu kaxa na da illa ga rayuwar ka ba, kai a kan ka kamata yae kasan hakan.
Matasan mu a wannan yanayin sun duqufa kacokam kan shaye shayen kayan mayen da xae fitar da su daga siffa ta kamala.
Duk mai shaye shaye walau mace ko namiji xaka same shi a cikin al'umma ya rasa wani gata da sauran nutsattsun al'umma suke samu.
Duk dan Shaye Shaye kallon mutumin Banxa ake mishi, Maras Tunani, kuma wanda bae da Wayo, Baya da Mutunci ko Kima a Idon Manyan Mutane Kamilallu ba Manyan Mutane masu babbar riga ba.
Akwae dalilae da dama da suke jefa matasan mu a irin wannan halin qa-qa-ni-kayi din nan
Talauci
Rashin Sanya Idanu a Tarbiyya
K'addara
Auren Dole ( Ga Mata )
Abokai x Qawaye Gurbatattu
Shaye Shaye na taka muhimmiyar rawa wajen durqusar da Lafiyayye ya dawo Gajiyayye ko kuma Matacce a raye.
Da ace Matasan mu xasu Farga su gane irin Illar da Shaye Shaye yake yi ga rayuwarsu da sun daina tun kafin ace musu babu Kyau.
MATASA A RAGE YAWAN SHAYE SHAYEN KAYEN MAYE KO DOMIN INGANTA LAFIYAR KU.......... LAFIYAR KA JARIN KA
S. I. Hashim Kunya
10th, June, 2018 C.E
24th, Ramadan, 1439 A.H
9:00am