TARIHIN KUNYA HEALTH FORUM 0.2

*💫 KUNYA HEALTH FORUM (K.H.F) ✨* 

 ⭐ ( K.H.F 002)  KASHI NA BIYU 2
 *Nasarorin da K.H.F ta samu tun bayan Kafuwarta acikin August, 2022.* 

💦🌧️ *Tasirin K.H.F ga al'ummar garin Kunya* 

1.) K.H.F ta jajirce domin tabbatar da garin Kunya ya samu asibitin kwanciya *(aqalla Cottage Hospital)* 

2.) Kulla kyakykyawar  alaqa tsakanin K.H.F da hukumomi da mahukunta amatakai daban-daban na kiwon lafiya dake ciki da wajen garin Kunya
 
3.) Bayar da shawar-shawarin kawo gyara acikin qananan asibitocinmu na garin Kunya (Ibrahim Kunya Model & Kunya PHCs)

4.) Sadaukar da lokutanmu domin aikin sa'kai na duba maras lafiya acikin qananan asibitocinmu *(K.H.F Volunteers Initiative)* 

5.) Rabon kayan tsaftar muhalli kyauta ga qananan asibitocinmu na garin Kunya 

6.) Kaddamar da shirin inganta tsaftace asibitocinmu na garin Kunya wata-wata daga watan January, 2024. *(PHCs monthly Sanitation)* 

7.) Shiryawa da gabatarda aikin duba maras lafiya abasu magani kyauta *(Free Medical Outreach)* wanda *Alh. Jatau Islamic Centre (AJIC)* take daukar nauyi duk Shekara(2022, 2023 da 2024).

8.) Kaddamar da shirin kacici-kacici a manhajar WhatsApp, mai suna *'Ramadan Bonus 2023'* don wayar dakanmu da  mutane afannonin kiwon lafiya.

9.) Ruwa-da-tsaki awajen Kira ko jan hankalin al'umma afannonin kiwon lafiyar al'ummar garin Kunya

10.) Aiwatar da wayar da Kai ga dalibai makarantun sakandire na garin Kunya *(Schools Health Education)* 

(11.) Bayarda kyautar magungunan kulawar gaggawa ga makarantun sakandire na garin Kunya ( *First Aid Box Drugs* )

12.) Kulla Kawance da sauran kungiyoyin matasa na cigaban cikin  garin Kunya.

13.) Shirya wasan kwallo na sada zumunta duk Shekara tsakanin K.H.F da Kungiyar malaman makarantun garin Kunya ( *Kunya Progressive Teacher's Forum)* 

14.) Kaddamarda gidauniya domin tallafawa qananan asibitocinmu na garin Kunya *(K.H.F Fund Raising Committee)* 

15.) Nemawa qananan asibitocinmu tallafi daga mawadatan garin Kunya domin inganta Kulawa ga maras lafiyanmu.

 ðŸ’«✨ *TASIRIN K.H.F GA YAN KUNGIYAR*  

1.) Munyi nasarar bude shafin sada-zumunta na whatsApp a tsakanin dalibai da ma’aikatan sama da 180 Yan asalin garin Kunya dake ko'ina afadin duniya.

2.) Samar da manhajar *Goggle Form* mai dauke da kididdigar bayanai na yan kungiyar K.H.F.

3.) Munyi nasarori afanin wayar dakan daliban kiwon lafiya bisa hanyoyin qarin karatu, tallafi ko  neman kwarewar aiki.

4.) Munyi nasarar shiryawa da gabatar da bitocin qarawa juna sani sama da goma(10) atsakanin K.H.F members ( *Health Cadre Presentation Series).* 

 ðŸ”¥ðŸ’¥ *Kalubalen da muke fuskanta wajen tafikar da K.H.F* 

1.) Qaranchin kudade domin cigaba da aiwatar da wadannan muhimman ayyuka, da wasu da muke da burin aiwatarwa nan gaba.

2.) Rashin samun cikakken dama ta lokaci wajen aiwatar da kudire kudiren K.H.F akan lokacin saboda yanayin ayyukanmu.

3.) Karanchin goyon baya  daga mahukunta, mawadata, da yan siyasarmu na wannan yankin

4.) Yawaitar mummunar akidar bani-na-iya, fifita siyasa, muqami ko bangaranci da suke dakile cigaban garin Kunya.

Alhamdullah, duk da wadannan Kalubalen, nasarorinmu sunfi yawa kuma cikin dan qan-qanen lokaci, ..Masha Allah 

Asaurari saqo na gaba

 *Signed:* 
CTC, Kunya Health Forum
Previous Post Next Post