YADDA AKE DOWNLOADING VEDIO A FACEBOOK CIKIN SAUKI.

YADDA AKE DOWNLOAD NA VEDIO A FACEBOOK BA TARE DA SHAN WAHALA KO BATA LOKACI BA.


Visit http://ibnhashimkunya.blogspot.com
or
https://Kunyatech.websites.co.in
or
Ibrahim Hashim Saad @Facebook

Kamar yadda mutane da yawa suke aiko mana da sakonnin tambayoyinsu musamman dangane da abinda ya shafi neman sanin yadda ake sauke Vedio daga facebook zuwa kan waya, wanda da yawan mutane gaskiya basu san yadda ake yi ba duk da suna ganin Vedios masu kyau da burgewa suna son ajjiye su a wayoyin su domin kalla a duk lokacin da suka bukata.

Alhamdulillah a cikin wannan rubutun zan koya muku wato zan nuna muku yadda ake sauke shi wannan Vedio zuwa kan waya.

Da farko duk vedio din da ka gani kake son sauke shi akan wayar ka zaka taba vedio din zai bude kamar kana kallo, daga sama gefen hagu akwai wasu alama kamar haka  ... da zaka gani sai ka taba wurin, idan ka taba zai bude maka contest na vedion  za ka ga items kamar haka

Pin post
saved vedio
edit post
who can comment on your post
edit privacy
move to archieve
move to trash
turn off notifications for this post
copy link.

to sai ka shiga Copy Link din sai ka taba zai copy akan wayarka, nasan kowa dai ya iya Copy and Paste a wayar android😌.

zaka bude Chrome din ka ko Vidmate in kana da ita sai kaje wajen download kayi Paste na wannan Copy link din da ka yo, zasu baka damar shiga shafin da ka ga Vedion na Facebook, kuma su baka damar yin download din shi zuwa kan wayar ka.

zaku iya yin download din ma ta cikin Xender din ku duk hanyoyin kusan iri daya ne sai dai yan Bambance da baa rasa ba.

Ibrahim Hashim Saad
Sat 15th July 2023.
08106565749.
Previous Post Next Post