YADDA AKE SAMUN KUƊI DA FOLLOWERS.....

 Bari na yi gwari-gwari game da maganar tara followers :


Ba ka mamakin me ya sa 'yan kwallo ke samun makudan kuɗaɗe? Saboda akwai masoya kallon kwallo ne da yawa, shi ya sa hankalin manyan kamfanoni ya karkata gare su, suke musu tallace-tallace, duba stadium, duba rigunansu, da irin zunzurutun kudin da ake zubawa don talla (sponsorship).


A ina'yan film ke samu makudan kuɗaɗe? Modelling, ambassadorship, duk yana da nasaba da yawan masu bibiyarsu, a yanzu kam gaba daya hankalinsu da harkokinsu sun dawo kan social media. Sai su film ko waƙa su ɗora a shafinsu ba tare da an yanka CD, ko siyar da shi a cassette ba (kamar a baya). Ba ka ganin tallace-tallace a Labarina da sauran films da Arewa24 ke ɗorawa?


Me ya sa malaman addini na Musulmai da Kirista ke da tasiri, har gwamnati ke shakkarsu don a zauna lafiya? Yawan mabiya shi ne jarin malami a Nijeriya.


Me ya sa a yau, manyan 'yan siyasar kasar nan ke rububin bin Kwankwaso? Yana mabiya, yana da tasiri a siyasar Nijeriya.


Babu yadda za ka tara followers ba tare kana da tasiri (influence) ba. Yaɗa abubuwan (contents) da kake ɗorawa a shafinka shi ne ja hankalin mutane su fara bibiyarka (following). 


Influencers a social media sun kasu kashi-kashi daga yawan mabiya:


1. Mega influencer (mai mabiya sama da 1million), yawanci celebrities ne 'yan film da mawaka, malaman addini ko 'yan siyasa, manyan 'yan kasuwa da philanthropists, a Facebook kamar Ali Nuhu Mohammed 3.4 (film actor), Davido 4.6M (mawaki), Muhammadu Buhari 1.2M (siyasa) da sauransu.


2. Macro influencer (masu followers 500k zuwa 1 million), a kan samu 'yan siyasa, mawaka da shaharrun mutane a kan aikinsu ko kasuwanci, a Facebook misali 


3. Mid-tier influencer (mai mabiya 50k zuwa 500k), yawanci masu amfani da social media ne yau da gobe, misali, Fadila H Aliyu 203k (marubuciya), Maryam Shetty 201k (siyasa), Fauziyya D. Sulaiman 142k (humanitarian), Sada Suleiman Usman 78k (ambassador), Uwa Aishatu Gidado Idris 75k (zamantakewa) da sauransu.


4. Micro-influencer (mai mabiya 10k zuwa 50k), misali Adamu Kazaure 30k (makaranci/marubuci), Anas Darazo 42k (dan kasuwa & marubuci) , Lihambal 13k (motivation), Badamasi Aliyu Abdullahi (kasuwanci) da sauransu.


5. Nano-influencer (mai followers 1k zuwa 10k), misali Ukasha Ismail 6k (tsaro), Sheikhul Hubby 7.7 (soyayya) da sauransu.


Mene ne amfanin tara mabiya a social media? Mu duba misalai wasu shafuka a kasa:


1. Misali, Sabinus yana da followers 3.1, idan ya ɗora 'content' 1, a ƙalla ya kan samu viewers 500k - 1m+


2. Idan ka buɗe 'content' nasa za ka ga talla, Facebook Ads CPM suna biyan kowanne 1k views a $14.9 (₦6,800), ka lissafi 1000 x 1000 nawa ne?


2. Duk wanda ya click akan link na tallar da ya ɗora, yana da $0.44 (₦203), ka lissafa adadi followers da zu click akan 'ad', koda da rashin sani.


3. Followers kan ba wa mutum star, misali duba shafin Lihambal, a safiyar yau 99 stars ₦495 ce, ka lissafa adadi followers da content ya burge su, za su ba ka star (kowacce star tana ₦5).


4. Idan kana wani kasuwanci a social media, kuma kana da tarin followers, da yawa cikin followers za su patronazing ka, misali ka duba shafin Zeefas (fashion design) a Instagram, Anas Darazo (hula) da Najib Muhd Salisu (data).


5. Masu ɗora contents da tarin followers sukan iya karɓar ambassadorship na kamfanoni domin talla. Idan Sabinus zai ɗora ma talla a shafinsa, sai ka biya shi 1.5m ko fiye, ya danganta da yanayin tallar (Creebhills, 2022), a 15th January, 2023 ya yi wa kamfani Eva Water talla (a hoto). Kwana 3 da suka wuce, Ali Nuhu ya ɗora tallar Yale, a baya ya yi wa Vento, Bournvita, Mouka, Zinty, Rafaidha, Top Tea da sauransu da yawa.


Wannan a iya Facebook kawai kenan. Ina ga Youtube, Instagram, TikTok da sauran social media platforms? A social media, wasu na samun miliyoyi.


✍️Aliyu M. Ahmad

7th Dhul qhidah 1444A.H


Previous Post Next Post